Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma'a, Gharibabadi ya ce: "Madadin Isra'ila ta yi hisabi a kan shigar da abubuwan da suka shafeta a cikin jerin Majalisar Ɗinkin Duniya game da cin zarafin fade mai nasaba da rikici, gwamnatin Isra'ila ta hukunta Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya – wanda wannan alama ce ta wannan mummunar dabi'a: gujewa hukunci ta hanyar kai hari ga cibiyoyin duniya".
Ya kara da cewa Isra'ila na ci gaba da dagiya kan yarjejeniyoyin tsagaita wuta da ake da su a Gaza da Lebanon, waɗanda har yanzu suka kasa dakatar da ayyukan hare-haren, gami da kisa, tashin bama-bamai, take hakkin ƙasa, da ƙaura ta tilas.
Jami'in na Iran ya nanata cewa cin zarafin fade mai nasaba da rikici, hare-hare kan fararen hula, da kuma kin bin yarjejeniyoyin tsagaita wuta akai-akai ya kamata a bincike su kuma a gurfanar da su a ƙarƙashin dokokin duniya a matsayin laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil'adama.
Gharibabadi ya bukaci ƙasashen duniya da su kawo ƙarshen "gujewa hukunci da gwamnatin mamaya ke yi".
Rubutun nasa ya zo ne bayan da aka bayar da rahoton cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ta saka sunayen cibiyoyin Isra'ila a cikin jerin baƙin layi na masu laifi da ke da alhakin cin zarafin fade a yankunan da ake rikici, bayan shekaru na rahotanni game da azabtarwa, wulakantarwa, da cin zarafin fade a cikin gidajen yarin Isra'ila da sansanonin tsaro na soji.
A cikin wani rubutu a shafin sadarwar zamantakewa, jakadan Isra'ila a Majalisar Ɗinkin Duniya, Danny Danon, ya mayar da martani kan matakin Majalisar Ɗinkin Duniya, yana cewa, "Wannan qudiri ne a siyasan ce! Da bas hi da alaƙa da gaskiya da halin da ake ciki!"
Ya kara da cewa Isra'ila ta gabatar da shaidu don karyata rahotannin Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam, rahotannin bincike, da shaidar waɗanda ake tsare sun rubuta tsawon watanni game da ƙaruwar rahotannin cin zarafin fade da wulakancin da sojojin Isra'ila ke yiwa da mazauna yankunan, da ma'aikatan gidajen yari suke yi, tun bayan fara yaƙin Isra'ila a Gaza a watan Oktoba na shekara ta 2023.
A watan Maris da ya gabata, Francesca Albanese, wakiliyar Majalisar Ɗinkin Duniya ta musamman kan yanayin haƙƙoƙin da ke faruwa a yankunan Falasdinu da aka mamaye tun 1967, ta ba da rahoton cewa "duka mai tsanani, cin zarafin fyade, musgunawa mai kisa, yunwa, da kuma hana mafi yawan abubuwan da suka shafi rayuwar ɗan'adam na yau da kullun sun haifar da raunuka masu zurfi na dindindin a jikuna da tunanin dubban Falasdinawa da 'yan uwansu".
Kamar yadda rahoton ya kawo,Tun watan Oktoba na shekara ta 2023, sace Falasdinawa a yankunan da aka mamaye ya "ƙaru sosai," tare da kama mutane fiye da 18,500, ciki har da aƙalla yara 1,500.
Sakamakon binciken da jaridar The New York Times ta yi, wanda aka buga a ranar 11 ga watan Mayu, ya kuma yi cikakken bayani game da zarge-zargen cewa sojojin Isra'ila, mazauna yankunan, da masu gadi na gidajen yari sun yi wa Falasdinawa da ake tsare fyade, cin zarafi ga yara, azabtarwa ta jiki, wulakantarwa, da sauran nau'ikan musgunawa.
………………………………………..
Your Comment